Jazuli Adamu Garko, edita kuma marubucin labari a masana’antar Kannywood- ya ce babban abinda ke ciwa editoci na masana’antar Kannywood tuwo a kwarya, bai wuce rashin bincike ga sana’ar ta su ba, domin su kara wa kansu ilimi duba da wayewar kai da cigaban zamani da ake da shi a yanzu.
Inda ya ce mafi yawan mutane basa amfani da wayoyin salula ta hannunsu domin duba karatu ta hanyar amfani da shafin Youtube, wajen nazarta cigaban da duniya ta samu mussamam ma ga su editoci domin su karawa kansu ilimi a fannin na editin.
Ya kara da cewa matsalolin da ake samu na rashin jonuwar hotuna ko rashin samun sauti a fina-finai dai ba laifin edita ba ne, wannan matsalar takan samo asali ne tun daga wajen daukar fim.
Jazuli ya kara da cewar, idan aka samu irin wannan matsala edita kan yi wasu yan dabaru amma a cewarsa, akwai lokutan da basa iya gyara shi sakamakon yadda aka dauko hoton fim tun da fari.
Ya ce amfanin wayar hasnnu ba kawai a saka mata data ba don shiga shafufufkan yanar gizo kamar su Facebook, twitter, ko Instagram da sauransu ba, maimakon haka a yi nazari da su.
DandalinVOA a karshe ya tambayi edita Jazuli ko me suke yi a kungiyance domin kawo gyara, ya ce wannan hurumin shugaban kungiya ce wajen kawo gyara a fina-finan da Kannywood ke fitarwa bayan editocin sun tantance fim.
Facebook Forum