Ali Haruna Abdallah, wanda aka fi sani da Maza, mawaki da ya shahara a fannin wakokin hip-hop, kamar yadda yake cewa ana isar da sako daban-daban, bata yadda sauran nau'ukan wakoki kanyi ba.
Maza ya ce yana wakar hip-hop ne sannan kuma wakokinsa sun fi karkata ne ga fadakarwa, da wa’azantarwa mussamam ma ga matasa domin su hankalanta ga yadda suke tafiyar da rayuwarsu a yanzu.
Ya samu alfanu da dama inda ya ce da waka yayi fice , wanda ficen ya haifar masa da samun tallace-tallace daga wajen al'umma kamar daga kamfanoni da dai daikun mutane domin yi musu talla.
Ya ce daga cikin kalubalen da suke fuskanta mawaka masu tasowa shine, bayan mawaki ya shiga mawuyacin halin tara kudin da zai yi recording din wakarsa, sai wani a can da bai san wahalar da mawaki ya shiga ba ya ce wakar ba ta yiba.
Ya kara da cewa sabbin mawaka irin wadannan kalamai na tauye su kafin daga bisani su fuskanci yadda abin yake, na cewar idan wani ya kushe maka waka wani kuwa yabon sa yake yi a wakar ta ka. Daga karshe Maza ya ce babban burinsa shine yayi fice a duniya.