Jama’a da dama sun ga amfanin shafukan yanar gizo musamman bayan rabuwa da abokai ko ‘yan uwa da basu taba tunanin sake ganin ba, amma ta hanyar wadannan shafuka na zamani, jama’a da dama sun sake sada zumunta tsakanin su da abokai.
Matasa a sassa daban daban na duniya sun sadu da abokan da basu taba gani ba, wasu sun sami abokan auratayya wasu kuma na harkokin kasuwanci. Amma abin tambaya a nan shine, ko jama’a na la’akari da illolin wadannan shafuka na sada zumunta na yanar gizo?
Masu iya Magana sun ce; a rika sara ana duban bakin gatari, wannan karin Magana ta zo dai-dai da irin yanayin da matasa maza da mata suka sa kawunan su musamman ta amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo.
Kamar yadda muka saba zantawa da da matasa samari da ‘yan mata akan yadda suke yawaita amfani da wayar hannu wajan amfani da shafukan sada zumunta, yawancin su basa la’akari da illar yawaita amfani da wannan fasahar zamani.
Ku biyo sati mai zuwa domin sauran tattaunawar
Facebook Forum