Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuzo Kasashen Afrika, Davido Ya Lashe Kyautar BET A Amurka


Fitaccen mawakin nan dan Najeriya wanda aka fi sani da Davido, ya lashe shahararriyar kyautar kasa-da-kasa ta wannan shekarar, a yayyin da yake karbar kyautar inda ya daga kambun da aka karrama shi da shi, ya bayyana jin dadin sa inda har ya shaida ma ‘yan kallo cewar “Akwai bukatar kuzo kasashen Afrika dominn ganin irin hazaka da matasa ke da ita a nahiyar.”

Ya kara da cewar “Ina shaida muku cewar muna da matasa masu hazaka a kowane bangare na rayuwa, don haka ya kamata kuzo don cin ire iren nau’ikkan abinci da kayan sawa da muke dasu a Afrika.”

Akwai mu da mawaka da zasu iya gogayya da mawakan duniya, wannan nasarar tawa ta kara harzuka matasa daga kowace a’lada, don haka akwai bukatar matasa su hada kansu waje daya don ganin sun samu nasara a kowace irin sana’a suka saka a gaba.

Sunan mawakin na asali shine David Adeleke, wanda ya doke mawakiyar nan Tiwa Savage, da mawakin kasar Congo Fally Ipupa, kana da mawakin kasar Ingila Stormzy, mawakin dai ya taba lashe wannan kayautar a shekarar 2014.

A dai dai lokacin karbar kyautar mawaki Davido mai shekaru 25, ya bayyana ta’aziyyar sa ta rasuwar dan mawakin nan na Afropop D’banj, wanda ya rasu a karshen mako.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG