Samuel Eto'o Ya Yi Murabus Daga Matsayin Shugaban FECAFOOT

Samuel Eto'o

Samuel Eto'o ya yi murabus daga matsayinsa na Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamaru (FECAFOOT).

Tsohon dan wasan na Barcelona da Real Madrid da Inter Milan ya yi hakan ne saboda rashin nasara da tawagar wasan ƙwallon kafar Kamaru ta yi a gasar AFCON da ke gudana a kasar Kwaddebuwa wanda ƙasar ta fita a matakin silli ɗaya kwale.

Amma kuma kwamitin zartarwa ya yi watsi da shawarar da Eto'o ya dauka kuma ya sabunta goyon bayansa ga tsohon ɗan wasan Indomitable Lions ɗin

Kamaru ta fita da gasar bayan tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke ta da ci biyu da nema a wasan zagaye na biyu na gasar na cin kofin nahiyar Afirka.

Ademola Lookman mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta Atalanta a kasar Italiya ne ya zura wa Najeriya kwallaye biyu.

Daya kafin a tafi hutun rabin lokaci a dai dai minti 41 na buga wasan, na biyu bayan an dawo hutu a misali minti 90 na wasan da ake bugawa a kasar Kwaddebuwa.