WASHINGTON DC, —
Sabuwar wayar Samsung Galaxy Note 9, na dauke da wani sabon tsarin manhaja, wanda zai sanar da mutun idan hoton da yake dauka yayi kyau, ko kuma kyamarar ba tayi seti dai-daiba.
Wannan wani sabon tsari ne da yake amfani da yadda mutun ke motsi da hannun su, kana sabuwar wayar bata tsaya kawai a wajen daukar hoto mai inganci ba, harma da yadda take tace hotuna da gyara su.
Ya zuwa yanzu kamfanin dai na kara kaimi wajen ganin ya inganta wayar tasa don wuce abokan gasarsa na kamfanin Huawei na kasar China. Wayar na da karfin batiri fiye da na sauran wayoyin kamfanin a baya. Za a fara sayar da wayar a ranar 24 ga watan Augusta. Wanda ake sa ran kudin wayar zai fara daga naira dubu dari hudu.