Muhimmiyar hanya guda da tafi dacewa domin isar da sako ga matasa masu sauraraon wakokin Hausa ita ce waka, kuma dalilin haka ne makasudin dalilin da ya sa na ji ina shi'awar waka, kuma gashi na sami kaina a cikin sana'ar a cewar mawaki Sammani.
A yayin da suke tattaunawa da wakiliyar dandalinvoa, matashin ya bayyana cewa yana wakokin da suka shafi harkokin ilimi, kuma yana mayar da hankali ne musamman ta wajan nusar da matasa yadda ake tura su makaranta domin neman ilimi amma sai a lokuta da dama sai sami kawunansu cikin wani hali na yawon da bai dace ba.
Sammani, ya kara da cewa ya kan rera wakokin al’amuran da suka shafi al'umma na yau da kullum, daga karshe ya bayyana cewa burinsa a harkar waka dai bai wuce ya ga jama’a a duk duniya na sauraron wakokinsa ba, kuma hakan na matukar yi musa amfani.
Daga karshe ya bayyana cewa babban abinda yake ci masa tuwo a kwayar shine yadda ya hada waka da harkar kasuwancin sa, wanda a lokuta da dama sana’oi biyun ke cin karo da juna.
Your browser doesn’t support HTML5