Sai dai mazauna yankin na cewa adadin ya zarta haka, ‘yan bindigar sun bude wuta a mahakar Zinarin wadda ke cike da hada hada, yayin da suka kashe mutane da yawa mafi akasari ma mahakan da ke cikin ramuka.
A cewar wani mazaunin garin yace gurin hakar Zinari guri ne da ake harkar makuden kudi, hakan yasa ‘yan ta’addar suka mamayi ma’aikatan suka kai musu hari wanda sakamakon hakan yanzu sama da mutane 40 sun rasa rayukansu daga jiya zuwa yanzu.
Kafin wannan hari dai ranar Lahadi maharani sun tare hanyar Dan Gulbi suna garkuwa da mutane hudu. Faruwar ire iren wannan tashin hankali ne yasa al’ummar Dan Sadau kowa ya zama dan aikin sa akai.
Kwamishinan yada labaru na jihar Zamfara, Umar Jibo Bukuyum, ya tabbatarwa da Muryar Amurka faruwar wannan lamari, inda yace tun lokacin da aka fara wannan tashin hankali gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci da suka hada da Kano da Katsina da Sokoto sun hada gwiwa don neman hanyar da za a kawo karshen wannan tashin hankali.
Wannan yanki na jihar Zamfara ya dade yana fama da matsalar kai hare hare da satar Shanu wanda a yanzu ya canza salo zuwa satar mutane domin neman kudaden fansa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5