Idan aka duba Najeriya dake zama babbar kasa mafi yawan bakaken fata a nahiyar Afirka, ‘yan kasar na ci gaba da bayyana ra’yoyinsu game da wannan zabe da ake gudanar
Akasarin ‘yan Najeriya dai sun karkata ne zuwa ga ‘yar takarar neman zama shugaban kasa Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat daga cikin ‘yan takara guda Hudu da ake dasu a Amurka.
Muryar Amurka ta zagaya a cikin birnin Lagos, domin jin ra’yoyin mutane da kuma dalilan da yasa mutane suka mayar da hankali ga ‘yar takara Hillary Clinton. Acewar wani dan Najeriya, shi dai yafi son Hillary Clinton saboda yawancin Amurkawa musamman ma talakawa sun fi nuna cewa ita suke so, haka kuma yana sha’awar ganin mata suna shugabanci musammanma a kasashen Turai.
Shima wani bawan Allah cewa yayi yana goyon bayan Hillary Clinton, domin ta fi kwarewa a harkar mulki kasancewarta Lauya kuma tsohuwar matar shugaban kasa, gata ‘yar Majalisar Dattijai har ma da wasu mukamai da ta rike.
Haka kuma ‘yan Najeriya sun nuna rashin goyon bayansu game da kalaman da Donald Trump ke yin a cewa ba zai bar wasu jinsin mutane da musulmai ba wajen shiga kasar Amurka.
Domin karin bayani.