Sama Da Kashi 60 Na Malaman Makarantun Jihar Neja Ba Su Da Ilimi - Gwamnan Jihar

Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri, 9 ga Satumba 2014.

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello ya ce sama da kashi 60 na malaman makarantu a jihar basu da ilimin koyarwa a makarantun.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani bikin yaye daliban cibiyar horas da ayyukan malunta ta Jihar Neja da ke garin da ake kira Dandaudu a karamar hukumar Sarkin Pawa. A cewarsa, akasarin malaman sun samu ayyukan ne ta fuskar siyasa ba wai cancanta ba.

"Kusan kashi 60 ko fiye da haka ma basu da kwararren ilimin koyar da yara," in ji Gwamna Sani Bello.

Ya ce hakan ya haifar da koma baya ta bangaren ilimi, amma duk da haka ba za a sallamesu ba.

Ya ci gaba da cewa, tun da suna da shawa'ar aiki, za a mayar da su cibiyar ta horas da malamai domin a ba su ilimin da za su iya koyarwa.

Shugaban hukumar bayar da ilimin bai daya ta jihar Neja, Alhaji Alhassan Bawa, ya ce bisa la'akkari da wannan matsala ta rashin kwararrun malamai ne yasa gwamnatin ta kafa wannan cibiyar domin samar da nagartattun malaman.

Kungiyar malaman makarantu ta ce ta amince cewa akwai malaman da basu kware ba wajen koyarwa sakamakon yadda suka samu aiki, amma sun nuna shakku kan yawansu ya kai da kashi 60 cikin dari da gwamnan ya bayyana.

Samar da ingantaccen ilimi wata babbar hanya ce na gina al'ummar da za ta kyautata makomar kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Sama Da Kashi 60 Na Malaman Makarantun Jihar Neja Ba Su Da Ilimi - Gwamnan Jihar - 2' 58"