Tawagar ta ba jam’iyyar wa’adin mako biyu ta dau matakin sauya Bankole ko kuma su mamaye shalkwatar.
A tsarin jam’iyyu dai a na samun matsayin shugaban nakasassu kamar yanda a ke samun na matasa da mata, inda nakasassun na zahiri a APC ke cewa an zabi lafiyeyye a matsayin wakilin su.
Yarima Sulaiman shi ya jagoranci ‘yan zanga-zangar ya na mai kira ga shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya dau matakin gaggawa kafin korafin ya ta’azzara.
Da ya ke maida martani, shugaban nakasassun na APC Tolu Bankole ya ce rashin fahimtar waye nakasasshe ya jawo korafin don ba sai an ga mutum ya na wargaje kafin ya zama mai nakasa ba.
“su na son ganin mutum ne a kan keken guragu, ko rike da sandunan tallafawa tafiya ko mutumin da a ke turawa a wulbaro, amma akwai bambanci don ni za a iya zaiyana ni a matsayin mai matsalar gani da ya sa na ke amfani da tabarau” inji Bankole.
Shugaban na masu nakasa a APC ya kara da cewa in a na shakkar ikirarin sa a tafi asibitin ido, in ya bude idon sa a ka duba, masu zargin za su ran ta a na kare.
Tawagar nakasassun karkashin Yarima Sulaiman ta taba zargin shugaban hukumar masu nakasa na kasa David Lalu da nuna bambanci wajen jagorancin sa, inda Lalun wanda ya taba rike wannan mukamin na APC kuma ya ke da nakasar rashin ji da kunne ya ce ba su fahimce shi ba ne, kuma kofar sa na bude ga duk nakasassu da alwashin gaiyatar su don tattaunawa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5