Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya daina jagorantar tattaunawar kasa da ake gudanarwa. Mataimakin shugaban dandalin Angelo Beda ya fada jiya alhamis cewa, shugaban kasar ya ajiye mukaminsa na uba, yanzu tsarin yana hannun al’ummar kasar Sudan ta Kudu.
WASHINGTON D.C. —
Karshen shekarar da ta gabata ne shugaban kasar ya shirya zaman tattaunawar da yace zai taimaka wajen kawo karshen rikicin da ake yi, da kuma shawo kan wadansu matsaloli da kasar ke fuskanta. Masu kula da lamura da dama a ciki da kuma wajen kasar sun kushewa shugaba Salva Kiir da sa kansa a matsayin shugaban tattaunawar da ya sanar a watan Disamba.
Beda yace lokacin da shugaban kasar ya rantsar da membobin kwamitin casa’in da biyu karshen watan da ya gabata, ya tsaida shawarar janyewa daga matsayin uba a kwamitin domin al’ummar kasar su sami karfin guiwa a shirin.