Rebecca Nyandeng ta shaidawa wani shirin tashar VOA dake harka fitila kan harkokin Sudan ta Kudu, “South Suda in Focus” cewa, rikicin cikin gida da shugaban kasar ke riba da shi, wanda tace yana azurta kansa, yayin da sojojin suke aiki ba tare da biyansu albashi ba.
“Ina rokon sojojin SPLA kada su yi fada da juna, su dawo a zauna lafiya, su daina wannan fadan rashin hankalin domin shugaba Salva, inji Nyandeng jiya Litinin.
Kungiyar SPLA, wadda tayi yaki domin kwatar yancin Sudan ta Kudu daga Sudan, rabu biyu tsakanin masu goyon bayan gwamnatin da kuma ‘yan adawa a farkon yakin da aka shiga a watan Disamba shekara ta dubu biyu da goma sha uku.
Nyandeng tace, idan sojojin gwamnati asuka ajiye makamansu, Salva Kiir ba zai iya ci gaba da mulki ba.
MDD tayi kiyasin cewa, sama da mutanen Sudan ta Kudu miliyan daya da dubu dari takwas suka kauracewa kasar zuwa wadansu kasashe tunda fadan y,a barke a shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Yayinda kuma wadansu miliyan daya da dubu dari shida suke gudun hijira a cikin gida.
Facebook Forum