Sallah: Ziyarar Jakadan Amurka a Cibiyar Addinin Islama a Nijar

Jakadan Kasar Amurka A Jamhuriyar Nijar

Jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijar Eric P.Whitaker ya ziyarci ofishin kungiyar addinin Islama ta kasa, domin isar da sakon taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar babbar salla, kokuma sallar layya wacce ake shagulgulanta a yanzu haka a kasashe da dama.

Wannan shi ne karon farko da wani babban jami’in diflomasiyar Amurka a Nijar ke kai ziyara a ofishin kungiyar addinin Islama, da nufin isar da sakon al’ummar kasar ta Amurka, musamman a irin wannan lokaci na shagulgulan salla.

Abin da ya kara gwada muhimancin mutunta addinin abokan zama a duk inda suke a duniya.

Ambasada Eric P. Whitaker, ya bayyana cewa da sunan gwamnatin Amurka yake yi wa al’umar musulmin Nijar barka da sallah.

Wannan wani lokaci ne na kara maida hankali ga ibada tare da yawaita addu’oi, sannan dama ce da ake taruwa wuri daya da iyalai, da aminai cikin yanayin zaman lafiya da kaunar juna.

Kasar Amurka kasa ce da kowa ke da ‘yancin yin addinin da yake so.

A Amurka, akwai akalla Musulmai miliyan 3.5.

Jakadan ya kara da cewa, sun yi amannar cewa, imani a addinance wani abu ne mai matukar muhimmanci a tsakanin al’umma.

Mutane masu nutsuwa da karfin Imani na taka rawa sosai a sahun al’umma abinda yake iya taimakawa sosai wajen samarda zaman lafiya, da yafewa juna, da kuma adalci.

Da yake karbar sakon al’ummar kasar Amurka, shugaban kungiyar addinin Islama, AIN ta kasa limamin babban masallacin Juma’a na birnin Yamai Sheik Jabri Oumarou Ismael, da sunan al’ummar musulmin Nijar, ya yaba da wannan yunkuri na gwamnatin Amurka.

Kasar Amurka na daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen tallafawa Jamhuriyar Nijar a yunkurin da kasar ta sa gaba wajen samar da zaman lafiya mai dorewa ta hanyar fadakar da shugabannin al’umma, da na addinai, da samar da aikin yi ga matasa.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Sallah: Ziyarar Jakadan Amurka a Cibiyar Addinin Islama a Nijar