Tsohon shugaban kasa Barack Obama ya nuna wani hoto ranar Asabar din da ta gabata a shafinsa na twitter bayan mummunan tashin hankalin da ya faru a birnin Charlottesville na jihar Virginia. Yanzu wannan sakon ya zama mafi farin jini a kafafen sada zumuncin zamani.
Hoton ya nuna shugaba Obama ya dafa karfen wata taga, rataye da rigar kwat dinsa, yana kallon wasu kananan yara masu launin fata dabam-dabam da suma suke kallonsa daga tagar.
Shugaba Obama ya rubuta “babu wanda ake haihuwa da kin jinin wani saboda bambancin launin fatarsa, ko kuma inda ya fito, ko addininsa. Hoton da sakon da Obama ya rubuta kenan, wanda asali tsohon shugaban Afrika ta kudu Nelson Mandela ne ya rubuta shi.
Wannan sakon na zuwa ne kwana daya bayan da wasu turawa suka yi zanga-zanga a birnin Charlottesville don nuna kin amincewarsu da matakin cire wani sassaken tsohon Janar wanda ya jagoranci dakarun ‘yan tawaye daga shekarar aluf dari takwas da sittin da daya zuwa sittin da biyar a yakin basasar da aka yi a Amurka. Wasu kuma masu adawa da wannan zanga-zangar suka dunguma kan tituna don nuna rashin amincewarsu da wadannan gungun mutanen, wani mutum kuma ya afka cikin masu zanga-zangar da mota, sanadiyar haka wata matashiya ta rasa ranta.