Sakataren Wikki Tourist Na Bauchi Ya Ba Zabgai FC Kyauta

A ranar Litinin 26/3/2018 ne sakataren kungiyar kwallon Kafa ta Wikki Tourist dake garin Bauchi, Alh Abdullahi Ibrahim Askiya, ya tallafa wa tsohon kulob dinsa zabgai International Fc Bauchi, rigunan wasa har iri biyu a shirye shiryen fara wasanni na NLO Division One Clubs 2017/18.

Da yake bada Kyautar Abdullahi Ibrahim Askiya, Marafan Chiroman Bauchi ya ce ya bada wannan tallafinne don ya taimaka wa tsohon kulob dinsa wanda ya taba rike mukamin sakatare a baya na tsawon shekaru tara

Kuma ya yi godiya ga wannan kungiya ta Zabgai inda ya ce duk matsayin da yakai a yanzu wannan kungiya ce sanadi. Daga matsayin da ya rike a Zabgai shine yasa aka bashi aiki a Gwamnatin jihar Bauchi sakamakon kwazonsa, har ya kai ga inda yake yanzu, don haka tarihinsa bazai cikiba sai an danganta shi da kungiyar Zabgai.

Ya yi kira ga Masu hanu da shuni da kuma gwamnatin jihar Bauchi da su taimaka wa wannan kungiya mai Tsohon tarihi wadda aka kafa ta tun shekarar 1976, kimanin shekaru arba'in da biyu a lokacin yana makarantar firamare.

A cikin tawagar da suka rako shi harda tsohon shugaban kungiyar ta zabgai Sadiq Yusuf Zariya, wanda yanzu mamba ne a kungiyar Wikki da kuma tsohon dan wasan kungiyar ta Zabgai, a shekarun baya da suka wuce Shehu Peter Inbachi, wanda duk kansu sun yi jawabai Masu ma'ana.

Shima Shugaban kungiyar marubuta Labarin wasanni na jihar Bauchi Nasiru Abdullahi Kobi ya tofa Albarka cin bakinsa.

Daga bisani Shugaban kungiyar ta Zabgai Alhaji Babangida Yalwa Jahun ya Gode wa Abdullahi Marafa bisa tallafin da ya kawo masu na rigunan wasannin har kala biyu ya ce ba wannan ne karon farko da Askiya ya fara taimakawa wannan kulob ba.

domin a baya ma yayi alkawarin amfani dashi ta yadda ya dace ya yi alkawarin samun nasara a kakanr wasan bana da ikon Allah

Cikin wadanda suka yi jawabi akwai Kaftin din Kungiyar Ibrahim Kanu, da kuma Shugaban Magoya bayan Kungiyar Abubaka Ahmed Yellow wadda suka nuna godiyarsu bisa wannan taimako da akai masu. Sunyi kira da a taimaki ‘yan wasan wajan haurawa dasu mataki na gaba a kungiyoyin kwallon Kafa kama daga jiha zuwa tarayya dama kasashen duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakataren Wikki Tourist Na Bauchi, Ya Ba Zabgai FC Kyautar Jesi