Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimanin 'Yan Wasan Super Eagles 18 Ne Suka Fara Atusaye A Filin Wasan Radisson


Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta tabbatar da cewa dan wasan tsakiya na Las Palmas, Oghenekaro Etebo ba zai samu damar halartar wasan sada zumunci da za'ayi da Poland ba amma zai tafi London a wasan da kungiyar zata buga da Serbia ranar 27 ga watan Maris.

Shima dan wasan Al-Ahly, Junior Ajayi kuma ba zai samu damar zuwa ba sakamakon bai sami takardar izinin shiga kasar ba wanda zai tashi kai tsaye zuwa babban birnin Ingila.

Dan wasan Tianjin Teda, kuma kyaftin din Super Eagles, John Obi Mikel bai iso ba har a jiya yana kokarin sabunta takardar izininsa wadda ana ganin zai yi wuya ya samu damar fafatawa a wasan farko da Poland ranar Jumma'a.

Sai dai 'yan wasan zasu samu shiga tawagar a wasan da Super Eagles, zata yi da kasar Serbia. kwana hudu bayan na Poland. dan wasa Ikechukwu Ezenwa, zai shiga cikin tawagar a ranar Laraba,

Kelechi Iheanacho, da Wilfred Ndidi, da kuma loanee Chidozie Awaziem sun isa sansanin horaswar da kuma Victor Moses.

Kimanin 'yan wasa sama da 18 suka samu hallartar sansanin horas da 'yan wasa dake Radisson Blu Hotel a Wroclaw Inda Kungiyar ta fara atisayen motsa jiki sau biyu tare da wadanda suka samu isowa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG