Sakataran Tsaron Amurka, Mark Esper, ya kai wata ziyarar da ba a sanar ba zuwa Afghanistan, a daidai lokacin da ake kokarin sake shiga tattaunawar zaman lafiya da kungiyar Taliban.
“Manufar hakan shi ne a cimma yarjajjeniyar zaman lafiya sannu a hankali, wato wata yarjajjeniya a siyasance, wanda hakan shi ya fi," abin da Esper ya gaya wa manema labaran da ke tafiya da shi kenan jiya Lahadi.
A watan da ya gabata, Shugaba Donald Trump, haka kwatsam, ya soke tattaunawar da Amurka ta ke yi da kungiyar Taliban lokacin da bangarorin biyu da ba su ga majici su ke dab da rattaba hannu kan wata yarjajjeniyar zaman lafiya, wadda da an yi da ta kawo karshen yakin na Afghanistan wanda aka kwashe shekaru 18 ana yi, wanda shi ne lokaci mafi tsawo da Amurka ta dauka ta na yaki a cikin wata kasar waje.