Carrie Lam, shugabar yankin Hong Kong, ta fada a yau Asabar cewa mutumin da ake zargi da aikata laifin kisa wanda batun sa ne ya janyo zanga zangar da ake yi a Hong Kong, saboda wani kudurin doka da zai ba Hong Kong din damar mika masu laifi Taiwan da kuma China, wanda Lam ta sanar da janye kudurin daga baya, Lam ta ce mutumin ya ce a shirye ya ke ya mika kansa ga hukumomin Taiwan.
Lam ta fadi cewa Chang Tong-Kai ya rubuta ma ta wasika, ya na cewa zai mika wuya ga Taiwan dangane da zargin sa da ake yi da hannu a laifin kisa.
Dama dai ana zargin Chang da kisan budurwarsa a Taiwan. Bayan da ya gudo daga Taiwan an damke shi a Hong Kong akan zargin laifin hallata kudaden haram amma ana sa ran za a sako shi kwanan nan.
Makonni 20 kenan a jere birnin Hong Kong ke fuskantar zanga zangar kin jinin gwamnati, bayan da a makon nan duka bangarorin biyu suka nuna cewa babu abinda zai canza.
Masu zanga zangar sun ce babu gudu ba ja da baya akan bukatocinsu guda 5 game da gwamnatin Hong Kong, ita kuma Lam ta ce ba zata biya bukatun masu zanga zangar ba.
Facebook Forum