Al'ummar kasar Kamaru sun ce kafin gudanar da zaen sun dauka Hillary Clinton ce zata ci ba Donald Trump ba.
Nasarar Donald Trump tamkar an zubawa mutane da yawa kasa a ido ne amma kuma lamarin ya kamata ya nunawa mutanen Afirka musamman Kamaru cewa dimokradiyar Amurka tana cigaba. Ba sai an yi wani magudi ba kafin a san wanda zai ci zabe.
Idan aka duba Afirka mafi yawan shugabanin nahiyar suna kan mulki na shekaru da yawa kamar ita kasar Kamaru inda shugabanta yake mulki yau fiye da shekaru talatin kuma yana son ya zarce a zame mai zuwa. Yakamata kasashen Afirka su yi koyi da Amurka. Misali Barack Obama yayi shekaru takwas yana mulki kamar yadda doka ta bashi yanzu zai sauka bai nemi "ta zarce ba".
Zaben Trump ya kamata yayi tasiri a nahiyar Afirka wajen kawo canji a harkokin shugabancin kasashe inda babu dimokradiyar kirki. Lokaci ya zo da 'yan siyasar Afirka ya kamata su bude ido su ga yadda dimokradiya ke gudana su kuma yi koyi domin su kawo canji a kasashensu.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5