Shugaba Buhari yace yana jinjinawa irin hanyoyi da tsare tsaren da kasar Amurka ta bi wajen tabbatar da cewa anyi zabe bisa ga tafarkin dimokaradiya wanda ya zama abin sha’awa ga duniya baki daya.
Kakakin shugaba Buhari a fadar gwamnati, Mallam Garba Shehu, kyakkyawar dangantar da aka samu kuma ta inganta tsakanin Najeriya da kasar Amurka a wannan mulki na shugaba Buhari. Wannan dangantaka ba kawai tsakanin mutum da mutum bace tsakanin kasa da kasa ce.
A kwai manufofi da suka hada Najeriya da kasar Amurka wanda suka hada da yaki da ta’addanci da yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta tattalin arziki. Game da wadannan manufofi Amurka da Najeriya suna da kyakkyawar fahimta.
Masani akan fannin difilomasiya Ambasada Adamu Sa’idu Daura, yace akwai taimako da Amurka ke yiwa Najeriya ta hanyar tsaro, inda take bada shawarwari a rikicin da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Haka kuma akwai dadaddiyar huldar cinikayya mai karfi tsakanin kasashen biyu, hakan yasa ‘yan Najeriya ke fatan idan sabon shugaban Amurka Donald Trump ya hau mulki zai ci gaba daga inda shugaba Barack Obama ya tsaya.
Domin karin bayani.