SOKOTO, NIGERIA - Da yawa ‘yan Najeriya dalibai ke tsallakawa zuwa kasashen ketare domin neman ilimi saboda wasu dalilai da watakila suka hana su neman ilimin a cikin gida Najeriya.
Wasu iyayensu ne ke daukar nauyin karatun nasu yayin da wasu kuwa gwamnatoci ne ke dauke da nauyinsu.
Ko ma dai wace hanya ake daukar nauyin daliban masana na ganin sakacin gwamnati a fannin kula da ilimi na daga cikin abubuwan da ke tilasta a fita ketare nemansa duk da wahalar da ke ciki.
A kwanan na wata tankiya ta bulla tsakanin gwamnatin jihar Sokoto da wani dalibi dan asalin jihar mai suna Yahaya Usman Gadabo wanda ke karatu a kasar Rasha.
Dalibin dai ya yi korafe-korafe wadanda wasu jaridu suka wallafa inda ya ke zargin gwamnatin Sokoto da kin biyan kudin karatun sa da ma zaman sa a kasar Rasha, abinda ya jefa rayuwarsa cikin kunci har ya fada hannun jami'an kula da shiga da ficen baki na kasar kuma a ko wane lokaci ana iya tuso keyar sa zuwa Najeriya.
A nata bangaren gwamnatin jihar Sokoto ta ce maganar da dalibin ya yi ba gaskiya ba ne, saboda tun shekarar 2014 ta soma daukar nauyin karatunsa a kasar Sudan da alwashin za a dauki nauyin karatunsa har tsawon shekara 5.
Bayan shekara daya ya koma kasar Rasha kuma an ci gaba da daukar nauyinsa har karewar wa'adin shekara 5, ya kuma nemi karin shekara daya aka kara masa, ya sake neman shekara daya aka sake kara masa.
Shugaban hukumar bada tallafin karatu wanda ya ajiye aiki kwanan nan Hassan Muhammad Rabah, wanda ya yi magana da yawun gwamnatin jihar ya ce binciken su ya gano cewa kudaden da gwamnatin Sokoto ke turawa yaron har ya sayi mota yana taxi kuma ya auri mata ‘yar kasar Rasha. Kokarin sake ji ta bakin dalibin ya ci tura.
Wani abu da ya dauki hankalin jama'a shi ne duk da fushi da gwamnatin tayi akan yaron ya bata mata suna, ta amince ta biya masa dukan kudin da suka rage na karatunsa, kuma tuni ta sauya wurin aiki ga daraktan da ke kula da lamurran dalibai masu karatu a kasashen waje na hukumar bayar da tallafin karatu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5