Sai ‘Yan Najeriya Sun Yi Zabe Nagari Sannan Ne Za A Iya Amfana Daga Dimbin Dukiyar Kasar - Masana

Magoya bayan yan siyasa

Masana na baiyana cewa sai ‘yan Najeriya a dukkan sassa sun yi zabe nagari ba da la’akari da wani bambanci ba ne za a iya samun cin gajiyar arzikin kasar mai yawa.

Bayanan masanan da masu sharhi na zuwa ne gabanin babban zaben Najeriya a ranar 25 ga watan gobe kamar yanda jadawalin hukumar zabe ya tsara.

Masanan na cewa duk matsalolin kasar da su ka hada da na tsaro da kuncin tattalin arziki za su kawo karshe idan masu zabe su ka duba wadanda su ka cancanta kama daga mukaman zartarwa da na majalisa.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr.Abubakar Umar Kari ya ce kama daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP da ke adawa ba sa marmarin duk sauye-sauye da a ka samu a dokar zabe da za ta iya yi mu su barazanar samun nasara kamar yanda a ka faro tun 1999.

Shi ma masanin kimiyyar siyasa na jam’iar Bayero Dr. Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce da zarar talakawa sun kaucewa son zuciya su ka samu dora jagorori nagari a zaben sun huta da kalubalen da ya ki ci ya ki cinyewa.

Shugaban kwamitin amintattu na gamaiyar kungiyoyin arewa Nastura Ashir Sharif ya ce duk matsalolin da ke addabar Najeriya na bayan tabarbarewar tsaro da in an dau matakan da su ka dace za a iya samun maslahar sauran matsalolin.

A tabaron Dr.Kari gwamnoni sun mamaye karfin wannan zabe na 2023 kusan fiye da kowane lokaci da har kungiyoyi su ke kafawa na cimma muradun su.

Wannan jamhuriya dai ta 4 ita tafi jan zare da samun shekaru 24 in an ma kwantanta ta farko da ta yi shekaru 6 ta biyu ta yi 4 inda sojoji su ka kifar da gwamnatin Shagari. Babban hafsan rundunar sojan Najeriya Lucky Irabor ya ce sojoji na mara baya 100% ga gwamnatin dimokradiyya.

Wannan na kwaranye barazanar juyin mulki da a ke fargaba matukar ‘yan siyasa su ka gaza hada kai.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Sai ‘Yan Najeriya Sun Yi Zabe Nagari Sannan Ne Za A Iya Amfana Daga Dimbin Dukiyar Kasar - Masana