Sai Da Aka Biya Kudin Fansa, Aka Sako 'Yan Kasuwar Jihar Kano

An samu nasarar sako wasu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa, wasu daga cikin Jami’anta sun rasa rayukansu a wata arangamarsu da ‘yan ta’adda, akan hanyar birnin Gwari zuwa Funtua, yayin da rahotanni suka inganta cewa, an sako ‘yan kasuwar nan na Kano da aka yi garkuwa da su, akan hanyarsu ta zuwa garin Aba ta jihar Abia bayan da aka biya kudin fansa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne ‘yan bindigar su ka yi kwanton bauna ga Jami’an da ke aiki a runduna ta 9 ta ‘yan sandan Najeriya masu aikin kwantar da tarzoma dake Kano, akan hanyar Birnin Gwari bayan kai gudunmawar aiki a wani bangare na jihar Neja.

Wata sanarwa a shafin twitter na rundunar ta ce jami’ai 16 ne ‘yan bindigar suka yi wa kwanton bauna suka kama su.

Koda yake, a cewar sanarwar, Jami’an sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, amma ‘yan sanda 4 sun mutu a yayin karanbattar, yayin da guda kuma ya bace.

Mai bincike Auwalu Bala, masani akan kimiyyar laifuka ya yi tsokaci kan al'amarin.

Hakan dai na zuwa ne, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, wasu ‘yan kasuwar Kano su fiye da 20 sun samu ‘yan cin su daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su, akan hanyar garin Aba na jihar Abia.

Bayanai sun inganta cewa, an biya kudin fansa kimanin naira miliyan 25.

Kaftin Abdullahi Adamu Bakoji, mai ritaya na bibiyar yadda harkokin tsaro ke tafiya a Najeriya, kuma ya tofa albarkacin bakinsa.

Yanzu haka dai galibin ‘yan kasuwar da suka kubuta daga hannun ‘yan bindigar, na karbar magani domin kuzarin jikinsu ya dawo yayin da suka ki cewa uffan ga manema labarai.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Sai Da A Ka Biya Kudin Fansa, A Ka Sako 'Yan Kasuwar Jihar Kano