Idan har bana jin ciwon kai, to zanji ciwon jiki, idan kuwa duk bana jin wadannan to ba shakka zanji ciwon gababuwa da na ciki, a cewar wata mata dake fama da wasu na’ikan cututtuka.
Amma tun daga lokacin da likitana ya bani wani magani da bani bukatar sha ko shafawa, gaskiya yanzu ciwon ya tafi. Likitan yana gudanar da wani bincike wanda yake amfani da wata na’urar da ake kira ‘VR in Hospital and Clinics.’
Ita dai na’urar VR tana daukewa mutum duk wasu zafin ciwo a duk lokacin da mutun yake famada su, domin kuwa takan kawar da hankalin mutum daga duk wani nau’i na radadi da mutum yake ji.
Ku Duba Wannan Ma Aure Baya Hana Neman Ilimi - Dr Maryam Sani AdoNa’urar dai akan rataya ta a wuya don kallon wasu abubuwa da ke faruwa a wasu duniyoyi, wanda hakan zai taimaka wa mara lafiya wajen kokarin ganin yadda za’a warware matsalolin dake a duniya, ta haka mutum zai manta da radadin ciwon da yake ji a jikin shi.
Marasa lafiya da dama da suka gwada wannan na’urar sun bayyana cewa, lallai ta taimaka musu wajen samun saukin radadin ciwon da suke fama da shi. Hakan na nuni da cewar na’urar zata taimaka wajen ganin mutane sun samu hanyar saukaka zafin ciwon dake damun su a kowane lokaci.