Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Da Wayar Hannu - Nakasu Ga Tarbiyya Da Harkokin Addini


A ci gaba da tattaunawar da muka fara makwannin da suka gabata akan matsalolin da yawan anfani da wayar hannu ke haifarwa ga matasa maza da mata musamman a kasashe masu tasowa, wani bincike da aka gudanar ba da dadewa ba ya bayyana yadda iyaye a kasashen da suka ci gaba suka nuna damuwar su akan yadda yawaita amfani da wayar hannu ke dauke hankalin 'ya'ya.

Baya ga daukar hankalin matashi ko matashiya, a lokuta da dama shafukan yanar gizo na budewa mai amfani da su ido a fannoni da dama da suka dace da ma wadanda basu dace ba.

Ta dalilin haka matasa da dama kan tsunduma cikin rashin tarbiyya, lamarin da masana ke hangen zai iya kawo nakasu ga harkokin addini da kokarin da iyaye ka yi wajan tarbiyantar da 'ya'ya, domin a cewar su, tamkar ana saka ne wani na warwarewa, wannan wani gagarumin aiki ne da ya kamata duniya ta farga domin shawo kan lamarin kafin ya yi mummunar illa.

Wasu daga cikin iyayen da suka bayyana yadda lamarin ke ci masu tuwo a kwarya sun nuna yadda hankalin 'ya'ya kan karkata a lokacin da suke amfani da wayar hannu musamman idan suna zance da abokai kokuma suna kallon hotuna ko ziyartar wasu shafukan yanar gizo, wannan yasa iyaye basa gane cikakken yanayin da 'ya'yan su ke ciki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG