Sabuwar Manufar Musayar Takardun Kudade A Najeriya Ta Jefa Fargaba A Zukatan Mutane

Dalar Amurka

A jiya litinin ne sabuwar manufar gwamnatin Najeriya kan musayar takardun kudade na Dala ta fara aiki, inda gwamnati ta tsame hannun babban bankin kasar CBN daga hada hadar cinikayyar kudin na Dala.

Sai dai ga alama sabuwar manufar ta jefa fargaba a zukatan masu kasuwancin mussayar kudi a wasu sassan kasar. wannan dai shine karo na uku da gwamnatin Najeriya ta kawo sabbin tsare tsare ko manufofi a bangaren musayar kudaden ketare cikin kasa da shekara guda, mataki na farko da gwamnatin da dauka shine dakatar da tsarin sayar da Dala ga kamfanonin ‘yan canji.

Sannan ta mika ragamar sayar da ita ga bankunan kasuwanci, amma daga bisani ta kawo tsarin hanasu kudaden Dala al’amarin da ya koma hannun babban bankin kasar baki daya.

Sai dai kuma a yanzu gwamnatin ta sake tunanin game da wannan al’amari inda ta bullo da sabuwar manufar tsame hannun shi kansa babban bankin kasar, kuma tace a yanzu farashin kudaden musayar na Dala kasuwace zatayi halinta amma ta hannun wasu bankuna guda bakwai da ta zaba.

A jiya ne dai wannan sabon tsari ya fara aiki a fadin kasar baki daya, sai dai hakan ya jefa kasar fargaba a zukatan ‘yan kasuwa da masu kamfanonin musayar kudade inji Adamu ‘Dan Juma Isah bakin Wafa, masu kamfanonin canji a jihar Kano.

Saurari rahotan Ibarahim Kwari daga Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabuwar Manufar Musayar Takardun Kudade A Najeriya Ta Jefa Fargaba A Zukatan Mutane 3'28"