Sabuwar Majalisar Wakilan Kamaru Na Yin Dammarar Aiki

Shugaban Kamaru Paul Biya a lokacin da yake daga wa magoya baya hannu a garin Yaounde. Satumba 15, 2011.

Yau Majalisar Dattijai sabuwa da aka kafa a kasar kamaru zata fara zamanta na farko.
WASHINGTON, D.C - Majalisar dattawan da ta kunshi mutum dari, na da 'yan majalisa su saba'in da aka zaba, ran 14 ga watan Afrilun da ta wuce, sannan ragowar talatin din, Shugaban Kasa ne ya zabe su da kanshi ran Larabar makon da ya wuce.

A wannan zama na farko ne majalisar zata tantance takardun karatu da shaidu na
'ya'yanta, sannan zata zabi wanda zai shugabanci majalisar.

Wakilin Muryar Amurka a can Kamaru, Mamadou Danda ya tattauna da Ibrahim Alfa Ahmed inda ya bayanna muhimmancin wannan zama na farko.

Your browser doesn’t support HTML5

Mamadou Danda Akan Sabuwar Majalisar Dattijai A Kamaru