Bayan ta samu rajista sabuwar jam'iyyar APC ta ce tana tattaunawa da gwamnoni 23 cikin 36 da kasar Najeriya take da su.
Bayan ta samu rajista sabuwar jam'iyyar APC ta ce yanzu haka ta kulla kawance da gwamnoni 23 ciki har da gwamnonin jam'iyyar PDP dake milkin kasar.
Mataimakin shugaban riko na sabuwar jam'iyyar mai kula da arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Umaru Duhu shi ya bayar da sanarwar kawancen a wani taron manema labarai da ya kira. Ya kara da cewa tuni sabuwar jam'iyyar ta soma ragistan sabbin mambobi kuma tun da ta samu gwamnoni 23 babu shakka jam'iyyar zata kafa gwamnati a shekarar 2015 idan ba wani canji Allah ya kawo ba. Da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya tambayeshi ya ambaci sunayen gwamnonin da suka shiga kawance da jam'iyyarsa sai ya ce abu ne na siri. Lokaci bai yi ba da za'a bayyan sunayensu. Sai dai wasu 'yan jam'iyyar CPC sun ce su a hade suke kuma haka suka shiga sabuwar jam'iyyar. Fatansu shi ne Allah ya sa wadanda suka hade dasu su yi adalci.
Sai dai wani malami a Jami'ar Modibbo a Yola ya ce sabuwar jam'iyya nada jan aiki a gabanta domin idan bata fitar da 'yan takara na gari ba to za'a koma gidan jiya. Ya ce idan 'yan siyasan da aka sani ne kuma damuwarsu itace su karbi mulki to da wuya.
Yanzu sai dai a sa ido a gani yadda wannan dambarwar siyasa zata kare a shekarar 2015.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5