Dokar, wacce aka ayyana a matsayin ta karfafa yaki da ta’addanci ta tanadi matakan kwace 'yancin zama dan kasa ga duk wanda aka kama da laifin ta'addanci.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya saka hannu kan dokar a ranar 27 ga watan Agustan 2024, wadda ta yi bayani kan jerin wasu abubuwan da idan dan Nijar ya aikata za’a saka shi a wani kundin rajistar mutanen da za’a tuhuma da laifin aikata ta’addanci ko kuma wadanda ke da nasaba da irin wannan aika-aika.
Alal misali, bai wa ‘yan ta’adda bayanan sirri ko yada wasu kalamai ko hotunan farfagandar ‘yan ta’adda ko kuma bayar da bayanai ga manyan kasashen duniya da ake zargi da daukan dawainiyar ta’addanci, ko fallasa sirrin kasa da yi wa tsaron kasa barazana na daga cikin tarin abubuwan da ka iya janyo wa mutum rasa matsayinsa na dan kasa.
A taron manema labaran da ta kira kungiyar kare hakkin bil adama ta Transparency International ta ce dokar ta saba wa alkawuran da Nijar ta dauka a kan batun kare hakkin bil adama, in ji shugaban reshen kungiyar Maman Wada.
Hukumomi na da hurumin kama dukiyoyi da kadarori ko kudaden ajiyar bankin dukkan wanda aka kama ko gungun mutane ko wata kungiyar da binciken ya tabbatar da samun su da laifin aikata abubuwan da dokar ta haramta da nufin karya lagon ‘yan ta’adda da masu taimaka masu ta kowace hanya.
Kungiyar Transparency na ganin wadannan matakai a matsayin wani yunkurin rufe bakin ‘yan kasa.
Malam Cherif Issoufou shi ne sakataren kungiyar mai yaki da cin hanci, ya ce wannan doka na iya hana yaki da cin hancin da rasha a cikin Nijar.
Sai dai hukumomi a ta bakin Ministan shari’a, mai shari’a Alio Daouda da ke karin haske a taron manema labarai, ya ce ‘’Ina tabbatar maku da cewa ko a matakin kasa da kasa, dokar na da tushe a shari’ance, idan aka yi la’akkari da kudirin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1373, wanda ya biyo bayan harin ta’addancin da aka kai a Amurka a 2001.
"Haka kuma kasashen Turai sun shigar da irin wannan tsari a dokokinsu kamar yadda wasu manyan kasashe irinsu Amurka suka kafa nasu dokokin cikin gida, don yaki da ta’addanci. A bayyane kudirin mai lamba 1373, ya bukaci kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya da suka yi na’am da yaki da ta’addanci su dauki matakai na hakika a shari’ance ko a hukunce don murkushe ta’addanci da ayyukan ta’addanci.
"Abin nufi ba’idin hukunce-hukunce da matakan shari’ah, an nemi kasashe su dauki matakan cikin gida makamantan wannan doka.”
A karkashin wannan doka, an bayyana cewa wani kwamiti ne ke da alhakin rubuta sunayen mutane ko kungiyoyin da ake zargi da kasancewa masu yada ayyukan ta’addanci a wani kundin musamman domin tantance ainahin makomar wadanda abin ya shafa, ma’ana ko hukunci ya hau kan su ko kuma a cire su daga jerin wadanda ake tuhuma, yayin da ta wani bangare dokar ta ce duk wanda bai gamsu da matakin da aka dauka kan sa ba na da ‘yancin shigar da kara a gaban kotu.
Sai dai wasu ‘yan kasa na ganin alamun an yi abin a dunkule ta yadda komai na iya faruwa a kan kowa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5