Shugaba Idriss Deby ya aika manzon mai suna Mohammed Alim Burba, wanda ya sami ganawa da shugaban Kamaru har na tsawon awa guda, inda suka tattauna kan dabaru na yakin da kasashen biyu ke fama da shi da maharan Boko Haram.
Kasashen Chadi da Kamaru sun dungukule guri daya domin hada karfi da karfe wajen yakar Boko Haram, kasar Chadi ta tura da dakarun tsaronta guda 2500 kan iyakar kasar jamhuriyar Kamaru domin yakar maharan, itama Kamaru ta jibge dakarun tsaronta sama da 5000 a jihar Arewa Mai Nisa kan iyakar kasar Najeriya da Chadi.
Da yake yiwa manema labarai jawabi Mohammed Alim Buba, yace “wannan ziyara dana kawo Kamaru, zai kara dankon zumunci kuma mun tattauna kan yakin da muke da Boko Haram, kana muna bukatar cewa zaman lafiya zai wanzu a tsakanin kasashen namu guda biyu.”
Domin Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5