Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar na fuskantar matsalar wutar lantarki


Jamhuriyar Nijar
Jamhuriyar Nijar

A daidai wannan lokacin kasashen yankin sahel ke fama da mugun zafin yanayi haka ma lamarin yake yanzu a kasar Nijar inda lamarin ya yi kamari domin ya hadu da karancin wutar lantarki.

A wannan lokacin zafi matsalar karancin wutar lantarki ta sa jama'a na kokawa a jamhuriyar Nijar.

To saidai kamfanin dake ba kasar wuta ya fitar da wani bayani akan matsalolin dake faruwa a tarayyar Najeriya kasar dake ba Nijar wutar lantarki. Akwai matsalar iskar gas da man da ake anfani dashi wurin samarda watar. Duk wadannan sun hadu ne da karancin wutar a tarayyar Najeriya kanta.

Matsalar karancin wutar da mugun zafin da jama'a ke fama dashi sun sa wasu a birnin Kwanni suna roko da sunan Allah da a agiza masu gameda matsalar ta wutar lantarki.

Wasu sun dogara ne da wutar su yi aikinsu kafin su samu abin da zasu tanadawa kansu da iyalansu abinci.Suna roko a tausaya masu.

Idan ma wutar ta samu cikin tsakiyar dare ake kawota lokacin da jama'a ke barci. Wata matsalar kuma ita ce yin anfani da kayan aikin da basu da inganci . Wasu da kamfani wutar kasar ta yi anfani dasu basa wuce kwana biyu kafin su fashe. Kenan koda an samu wutar ba zata kaiga jama'a ba domin gurbatattun karafa da wayoyin da ake anfani dasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG