Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukola Saraki Na Samun Goyon Bayan Yan Majalisun Najeriya


Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki

Batun shari’ar shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, shine kan gaba da za a iya cewa a yanzu jami’in siyasar Najeriya mafi girman mukami da yake fuskantar tuhumar rashin bayyana kadarori a bayanan dake gaban kotun da’ar ma’aikata wato Court of Conduct.

Wannan dai bai kai ga fara batun zargin ci gaba da karbar albashin watanni bayan sauka daga Gwamnan Kwara ba, da sabuwar maganar kwarmata ta Panama Papers. Shin wannan zai kai ga murabus din Sarakin?

Ga magoya bayansa a Majalisar da suka hada da kusan duk ‘yan PDP da akasarin ‘yan APC, na cewa ko hakan zai faru ba dai ta hanyar kuri’ar tsigewa ba, kuma ko Sarakin ya ga tsanantar lamarin shi zai canko wanda zai maye gurbinsa, kuma ba lalle bane ma ya zamanto dan APC ne ba.

Sanata Isah Hamma Mai Sahu, na kan gaba a masu mara bayan, inda yace badan Saraki ya zama Shugaban Dattawa da babu wanda zai shi, ya kumace banda Tinibu babu wani a APC wanda yayi aikiwa APC kamar Bukola Saraki.

Ga dai zargi iri-iri kan jami’an siyasa Sojoji da ma’aikatan Gwamnati, ga kuma tsarin bada baili da zargin bada cin hanci kan hanci. Ga gajiyawar talakawa wajen jiran ranar da Fetur da Wutar Lantarki dana kashewa a aljihu zasu inganta.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG