Sabon zababben Firayim Ministan Malaysia Mahathir Mohammed ya dakatar da babban atone-janar na kasar a shirye shiryen da yake na sake bude wani bincike mai alaka da asusun saka hannun jarin kasar da ake kira 1MBD.
Mahathir ya bayyana a yau litinin cewa zai maye gurbin babban lauya Apandi Ali, wanda ya wanke tsohon Firayim Mintan kasar Najib Razak daga kowanne irin laifi a cikin almundahanar da akayi a shekarar 2016.
Hukumomin Amurka sun ce jami’an 1MBD sun yi wadaka da kudin assusun wanda yawan su ya kai dalar Amurka biliyan 4.5 wanda aka samu wasunsu a cikin asasun Najib na banki. Najib wanda shine ya shugabanci bangaren bada shawarwarin asusun ya musanta duk wani zargi da ake mishi.
Har ila yau Mhathir ya sauke Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Dzulkifil Ahmad wanda Najib ya nada a shekarar 2016.
Firayim Minista Mahathir ya kuma sakawa Najib da Matar shi Takunkumi kan fita daga kasar bayan da aka samu rahoton cewa Najib da matar shi sunyi niyyar barin kasar zuwa Jakarta a wani jirgin da ba na haya ba a ranar Assabar din shekaranjiya.