Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Ya Hallaka Sama Da Mutane 40 a India


Irn barnar da ruwa ya yi a India
Irn barnar da ruwa ya yi a India

A arewacin India mutane sama da 40 ne suka mutu sakamakon ruwan sama mai karfi da guguwa mai fatiyar kilomita 70 cikin sa'a daya

Mutane sama da 40 sun mutu a arewacin India sakamakon wata guguwa mai cike da kura da ruwan sama mai karfin gaske da yazo tare da tsawa.

Tsawan da yazo hade da iska mai karfin gaske da yake tafiyar kilomita 70 cikin sa’a guda ya auka wa wannan yankin a jiya Lahadi wanda yayi dalilin rushewar gidaje tare da tunbuke itatuwa da kayar da itatuwa samar da hasken wutan lantarki a wuraren da suka hada da Uttar Pradesh,Andhra Pradesh, har zuwa kudancin Bengal, da kuma yankin Delhi.

A babban birnin kasar ko New Delhi iska ne mai tafiyar kilomita 100 a cikin sa’a guda yasa tilas aka karkatar da tafiyar jiragen sama har 70, kuma ya tilasta kulle babban filin jirgin saman kasa-da-kasa na Indira Ghandi har na tsawon sa’oi biyu, inji jamian aiki gaggawa.

Tun da farkon wannan watan an samu kwatankwacin irin wannan balai’in wanda yayi dalilin mutuwar mutane a kalla sama da 150 kana kusan dari 2 suka samu rauni iri daban-daban ajihohi 5, yayin da hakan yasa tilas aka rufe makarantu da dama a wasu gundomomi,

Wannan tsawar da iskan mai karfin gaskeba abu ne daaka saba gani akasar ta india ba musammam a irin wannan yanayin shekarar

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG