Shugaban da ya sauka a Jigawa da misalin 10 da rabi na safiyar Litinin, ya shiga jirgi mai saukar ungulu zuwa Auyo inda ya kaddamar da aikin sabunta nomar rani da ke karkashin kulawar hukumar Hadejia da Jama'are sannan ya wuce fadar mai martaba Sarkin Hadejia domin su gaisa.
Ana sa ran da maraice zai dawo birnin Dutse domin zuwa gaisuwar ban girma a fadar Mai Martaba Sarkin Dutse sannan ya kaddamar da aikin ruwa mai amfani da hasken rana wato Solar da gwamnatin jihar Jigawa ta yi.
Wani bafillatani makiyayi da ke zaune kusa da inda za a kaddamar da aikin ruwa na solar ya bayyana gamsuwarsa da ziyarar shugaban da kuma damuwarsa.
"Gaskiya abubuwan da mu ke bukata daga shugaba Buhari na da yawa, musamman ma mu Fulani saboda muna cikin halin matsi kamar wajen kiwo da mashaya," inji shi.
Ana sa ran Shugaba Buhari zai gana da masu ruwa da tsaki a jihar bayan liyafa a fadar gwamnatin Jihar Jigawa.
Saurari cikakken rohoton Mahmud Ibrahim Kwari
Facebook Forum