Shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko, yace sabon shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya tado da batun “tsokanar da Rasha ke yi musu, da kuma mamayewar haramci da tayi wa yankin Crimea” a hirar da suka yi ta wayar tarho da juna jiya Alhamis.
WASHINGTON DC —
A wata ganawar hadin-gwiwa da manema labarai da yayi a birnin Brussels tareda Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk da Shugaban Hukumar Kasashen Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ne Mr. Poroshenko yake cewa yayi wa Donbald Trump cikakken bayani dangane da halin da ake ciki a gabashin kasarsa da kuma a can yankin na Crimea.
Magangannun da aka ji suna fitowa daga bakin Donald Trump a lokacinda yake yakin neman zabe sun nuna alamun cewa idan ya ci zabe, zai sauya alkiblarsa zuwa yin aiki wajen inganta dangatakar dake tsakanin Amurka da Rasha.
Musamman Trump ya sha fitowa yana yabon shugaban Rasha din, Vladimir Putin, kuma yana caccakar Hilary Clinton saboda tana sukar lamirin shi Mr. Putin din.