Sai dai masana sun ce amfani da fasahar sadarwa ta zamani nada muhimmmanci wajen farfado da martabar tsarin aikin gwamnati a jihar.
Bayan rantsar da shi a dandalin Sawaba dake tsakiyar birnin Dutse a shekaranjiya Litinin, sabon gwamnan na Jigawa Alhaji Umar Namadi ya nanata aniyar sa ta aiwatar da kudirori 12 dake kunshe a daftarin alkawuran da ya yiwa al’umar jihar, amma ya ce garanbawaul ga tsarin aikin gwamnati shine abin da zai fara da shi.
“Sai mun fara da farfado da martabar aikin gwamnati da samar da yanayi mai kyau ga ma’aikata da kuma ba su horon daya kamata, san nan zamu sami sukunin aiwatar da manufofin mu dake kunshe a Ajandar mu ko kudirorin mu guda 12 ta hannun kwamishinoni da sauran manyan jami’ai da zamu nada”
Tuni dai kungiyoyin rajin ci gaban al’uma dana tabbatar da shugabanci na gari a jihar ta Jigawa suka fara tsokaci akan wannan furuci na sabon gwamnan na Jigawa.
Comrade Salisu Mazge Gumel na gamayyar kungiyoyin ci gaban al’uma a jihar Jigawa ya yi maraba da wannan yunkuri na sabon gwamna, amma ya bukaci gwamnan ya yi nazari akan tsarin tarbiyya daya tabarbare a tsakanin al’uma, yana mai cewa, galibi Jama’a a jihar ta Jigawa na kokawa akan yadda tarbiyya mai inganci ta yi karanci, musamman a tsakanin matasa.
Sai dai, amfani da ilimin fasahar sadarwa ta zamani wajen gudanar da sauye sauye ga tsarin aikin gwamnatin da sabon gwamnan ke fadi, shine abin da ya dace, a cewar Malam Sani Ahmed Kazaure, Malamin Ilimin fasahar sadarwa ta zamani a Jami’ar tarayya ta Dutse fadar gwamnatin Jigawa.
“A yau duk maganar da ake ta ta’allaka ne akan wannan harka ta ilimin fasahar sadarwa da injinan Komfuta, kuma muddin gwamnan yana da sha’awa babu abin da ya kamata a maida hankali a kai illa wannan harka ta ICT wato ilimin fasahar sadarwa ta zamani, hatta a akan batun yunkurin sa na garanbawul ga tsarin aikin gwamnati”
Baya ga tsarin aikin gwamnati, sabon gwamnan na Jigawa ya sha alwashin wadata manoman jihar da kayayyakin gudanar da ayyukan su na Noma, kamar iri da takin zamani da kuma motocin noma, a matsayin matakin habaka tattalin arzikin jama’a a sassan jihar.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5