Sabon Frai Ministan Pakistan Ya Yi Damarar Yaki Da Rashawa

Imran Khan Sabon Frai Ministan Pakistan

Shahararren dan wasan Cricket na duniya, Imran Khan ya daukin rantsuwar kama aiki a matsayin Frai Ministan Pakistan na cikon 22 a yau Asabar.

Sai dai zai huskanci kalubaloli da dama da suka hada da durkushewar tattalin arziki da kuma matsin lamba dake karuwa a kan kasar ta yaki kungiyoyin yan ta’adda da ake zaton suna gudanar da ayyukansu a kasar.


A cikin jawabin fara aikinsa biyo bayan zabensa da aka yi zuwa majalisar dokoki wuni guda kafin rantsar da shi, tsohon keptin wasan cricket din ya yi alkawarin tabbatar da matakan lissafi masu tsauri a kan masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa.


Khan ya yi nasarar samun mulkin ne bisa ga alkaura da ya yi a lokacin yakin neman zabe, cewa za a baiwa kowa hakkinsa daidai wadeda ba kamar yanda aka saba fifta wasu a cikin kasar ba. Wadannan kalamansa na kawo sauyi da gina sabuwar Pakistan sun yi tasiri wurin samun jama’a, ciki har da mazauna yankunan birane masu ilimi, da ma matasa masu ilimi, wadanda suke kallon gwamnatocin baya da cin amanar 'yan kasa.

Babbar kalubalen da wannan sabuwar gwamnatin zata huskanta shine yanda zata tsame kasar daga biyan bashin dake neman hadiye kasar. Masana tattalin arziki sun yi hasashe cewa sabuwar gwamnatin na bukatar daukar matakin gaggawar neman taimako daga hukumar lamuni ta duniya ta IMF, ta ceto kasar da kudade da zasu kai dala biliyon 14.


Sai dai sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yiwa hukumar lamunin ta IMF kashedi a cikin wannan lokaci ta daina amfani da kudaden harajin Amurkawa tana baiwa Pakistan ta biya basussukar da ta karbi a hannun China.