Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mummunar Hari Da Taliban Ta Kai Ya Kashe Sojoji 40


Jami'an tsaro a Ghazni
Jami'an tsaro a Ghazni

Wani samame a cikin dare da mayakan Taliban suka kai a tungar sojoji a arewacin Afghanistan ya haddasa kisan ma’aikatan tsaro 40.

Wani jami’in tsaro da bai yarda a bayyanar da sunansa ba a gundumar Baghlan, inda lamarin ya auku, ya fadawa Muryar Amurka cewa Dakarun kasar Afghanistan na rundunar ANA guda 31 da yan sanda tara suna cikin wadanda suka mutu.

Wani mai Magana da yawun kungiyar ‘yan tawayen yace a lokacin harin, sun kuma kame tungayen sojoji guda biyu, sannan kuma sun hallaka sojan Afghanistan 70, koda yake sau da yawa ‘yan Taliban din sukan yi karin gishiri a duk wani adadi da sukan bada.

Wannan harin na zuwa ne kwana guda bayan da Taliban ta kwace wani muhimmiyar tungar dakarun Afghanistan ta ANA a kusa da gundumar Faryab, suka kashe sojoji da dama kana suka kama wasu.

A hali da ake ciki kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kashedi a yau Laraba cewa fadan da aka kwashe kwanaki ana yi a kudu maso gabashin birnin Ghanzi, ya haddasa tsananin kunci rayuwa a kan fararen hula.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG