Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin Shuwagabannin Hukumomin Tsaro 12 Na Amurka Sun Yi Wa Trump Taron Dangi


Wasu giggan tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro sha biyu na Amurka sun yi wa shugaban Amurka Donald Trump taron dangi, suna la’antar shi kan matakin da ya dauka na soke alfarmar sani assiran kasa da ya cire wa tsohon shugaban Hukumar CIA, John Brennan a shekaranjiya Laraba.

A cikin sanarwar da suka bada jiya Alhamis mai dauke da sa-hannayen tsofaffin jigogin tsaron kasar da suka hada da tsofaffin shugabannin ita kanta CIA guda shidda da wasu tsofaffin mataimakan shugabannin CIA guda biyar da kuma

wani tsohon shugaban Hukumar Tsaro ta kasa, sun ce matakin da shugaba Trump ya dauka akan Brennan da kuma barazanar daukar makamancin matakin akan wasu tsofaffin jami’ai, ba ya da wata alaka da zancen ko waye ya cancanta ya sami masaniya game da assiran kasa, illa kawai magana ce da ta shafi ‘yancin fadar albarkacin baki.

A can wani gefen kuma, wani kwamandan sojan ruwa na Amurka da ya jagoranci sojan da suka kashe tsohon madugun kungiyar al-Qaida, Osama Bin Laden, ya fito fili, yana neman shi ma shugaba Trump ya soke tasa alfarmar ta sanin assiran kasar.

A wasikar da ya aikawa shugaba Trump, wacce aka wallafa a jaridar Washington Post, Admiral (mai ritaya) William McRaven yace raba shi da wannan alfarmar zai kasance kamar wata “karramawa” ce da za’ayi mishi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG