Sabon Bidiyon Shekau Ya Haifar Da Ce-ce-Ku-ce

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Biyo bayan fitowar sabon faifan bidiyo daga shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, masana na ganin tabbas gwamnatin Najeriya ta shiga gaban kungiyar a yakin da akeyi.

A cikin faifan bidiyon, Shekau ya musunta ikirarin da shugaba Mohammadu Buhari yayi na cewa sojojin Najeriya sun kore ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa baki ‘daya.

Shekau yace suna nan da ransu da lafiyarsu, kuma babu wanda ya kore su daga inda suke. Kamar yadda ya saba fitowa a kowanne faifan bidiyo ya fito ne zagaye da mayakansa dauke da bindigogi kuma fuskokinsu a rufe, a cikin bidiyon mai tsawon minti 25.

Wannan na zuwane a lokacin da gwamnati da rundunar sojan Najeriya ke ayyana nasara kan kungiyar Boko Haram.

Masani kan harkar tsaro Kabiru Adamu, yace Shekau ya fitar da wannan bidiyo ne saboda yunkurin da gwamnatin ta yi, idan kuma aka duba tsari na yaki wannan abu ne mai kyau. kuma ya kamata gwamnatin Najeriya ta nemi masu bincike su duba ta inda wannan bidiyo ya fito.

Domin karin bayani saurari hira da masanin tsaro Kabiru Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Bidiyon Shekau Ya Haifar Da Ce-ce-Ku-ce - 2'40"