Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samar Da Zaman Lafiya Mai Dorewa Shine Ya Rage wa Sojoji a Maiduguri


Maiduguri
Maiduguri

Rundunar sojan Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri, tace yanzu haka ta kammala yakin da take yi da kungiyar Boko Haram, abin ya rage mata shine samar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Janal Lucky Irabor, shine ya shaidawa manema labarai hakan, inda kuma ya gargadi jama’a da su guji baiwa mayakan Boko Haram mafaka, kuma yace yanzu haka suna nan suna neman mayakan a duk inda suke.

Irabor, yace a ranar 20 ga wannan wata rundunar ta su ta kame wani mai suna Abdullahi a kauyen Zabamari dake karamar hukumar Jere, tare da wasu mataimakansa wanda bincike ya nuna cewa an asalin kasar Burkina Faso ne. haka kuma a ranar 26 ga wannan wata ne suka sake kame wasu mutane biyu a cikin garin Maiduguri da taimakon bayanan sirri da sojojin suka samu.

Kwamanda Irabor dai yace yanzu ba zasu yi tsammanin komai ya kare ba, amma dai an karya lagonsu domin an lalata maboyarsu da kuma tarwatsasu.

Yanzu haka dai al’ummar jihar Borno na ta bayyana farin cikin su game da tarwatsa maharan da rundunar sojan ta yi a dajin Sambisa, wanda kuma shine ‘daya daga dazuka da ake ce mayakan sun tare a ciki.

Domin karin bayani saurari rahotan cikakken rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG