A cewar kakakin fadar shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, lokacin zuwan shugaba Mohammadu Buhari sun tarar ana biyan albashi na ma’aikatan gwamnatin tarayya zunzurun kudi Naira Biliyan 151, amma bayan wani bincike da ya kai ga cire ma’aikatan bogi dubu 50 albashin ya dawo Naira Biliyan 138 a duk wata.
Hakan na nufin a baya duk watan duniya ana wawure Naira Miliyan dubu 13 a bangaren albashi kadai na ma’aikatan da babu su.
Mallam Garba Shehu, yace daga watan biyu na wannan shekarar zuwa wannan watan da muke ciki na disamba an sami tabbacin cewa an toshe kofar da ake sace kudin gwamnati wajen biyan ma’aikata.
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Kwamarad Ayuba Wabba, yace bai kamata ba a tsaya a nan ba, ya kamata ayi bincike domin gano su waye ke karbar kudin. Ya kara da cewa irin wannan na faruwa amma ba a ci gaba da binciken don gano su waye ke da hannu.