Bayanan da muka samu daga bangaren Fulani na cewa maharin ya farma matasan fulani ne dake kiwo ya harbe shi a wuya da bindiga, ya rasu.
Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Bassa, Alhaji Ya’u Idris ya ce an kashe yaron ne ba tare da ya yi barna ko tashin hankali ba.
A bangare guda kuwa, mai magana da yawun kungiyar kabilar Irigwe, Davidson Malison ya ce an kashe mutane hudu ne yayin da suke aikin neman halal din su
Kakakin shugaban ‘yan sandan jihar Filato, ASP Gabriel Ubah ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin, wanda ya ce tuni suka tura jami’ansu don samar da taso a yankin.
jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta sha fama da matsalar rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci.