Hakazalika, wani jami’in hukumar kwana-kwana da ke kokarin aiki a wurin da ambaliyar ruwa ta auku a jihar Lower Austria ya mutu, a cewar mataimakin shugaban kasar Austria Werner Kogler ranar Lahadi ta shafin X, yayin da hukumomi suka ayyana lardin da ke kewaye Vienna, wanda ya hada iyaka da Jamhuriyar Czech da Slovakia, a matsayin inda iftila’in ya fi muni.
Koguna sun balle kama daga kasar Poland zuwa Romania, inda aka gano gawarwakin mutane hudu a jiya Asabar, bayan da aka shafe kwanaki ana tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Wasu sassan Jamhuriyar Czech da Poland sun fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni da aka gani cikin kusan shekaru 30.
A Jamhuriyar Czech, kashi daya cikin hudu na gidaje miliyan ba su da wutar lantarki saboda iska mai karfin gaske da ruwan sama. 'Yan sandan Czech sun ce suna neman mutane 4 da ke cikin wata mota da ta fada kogin Staric a kusa da garin Lipova Lazne mai tazarar kilomita 235 gabas da babban birnin Prague a ranar Asabar.
A kasar Poland kuma, mutum daya ya mutu a garin Klodzko, inda Firai Minista Donald Tusk ya ce shi ne yankin da bala'in ya fi shafa a kasar, inda aka tada mutane 1,600 daga yankin.
"Lamarin ya yi matukar muni," a cewar Tusk a ranar Lahadi a lokacin da yake magana da manema labarai bayan wani taro da ya je a garin Klodzko, wanda sassan sa ke cikin ruwa sosai yayin da ruwan kogin yankin ya kai tsayin santimita 665 a safiyar Lahadi.
Yawan ruwan ya zarta na tarihi da aka gani a mummunar ambaliyar ruwan da ta auku a shekarar 1997, wacce ta lalata sassan garin tare da kashe mutane 56 a Poland.