Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta yi tir da rusa ofishinta da aka yi a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta, Debo Ologunagba, PDP ta kwatanta rusa ofishin nata a matsayin tsokana, tana mai cewa hakan, alama ce gwamnatin APC da ke mulkin jihar na fargabar cewa PDP za ta kwace mulki a 2023.
“Gwamna Inuwa Yahaya ya tsorata da ofishin kamfen din PDP a jihar ta Gombe, wanda ya zama mahadar jama’a a wani yunkuri na kwato jihar daga gwamnatin APC.
Ku Duba Wannan Ma Na Yi Murabus Daga Shugabacin Kwamitin Amintattu Na PDP Don Kawo Sulhu – Walid Jibrin“Saboda haka, jam’iyyar PDP na kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta yi maza-maza ta sake gina mana ofishin kamfen dinmu tare da neman afuwa daga al’umar jihar. Sanarwar ta Ologunagbo ta ce.
Jam'iyyar APC ce ke mulki a jihar ta Gombe karkashin Gwamna Inuwa Yahaya.
Yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi, shugaban hukumar kula da tsarin birnin Gombe Peter Bilal, ya ce rushe-rushe da suke yi, ba su da nasaba da siyasa, illa kokari ne ake yi na tabbatar da an bi tsarin jadawalin birnin kamar yadda aka tsara tun a 2001, a cewar jaridar Vanguard.