Rundunar 'Yansandan Jihar Oyo ta Cafke Wasu Gaggan Matsafa

Hukumomin tsaro

Cikin 'yan kwanakin nana aka gano wani daji kusa da Ibadan inda wasu ke boye mutanen da suka sata suna kashesu domin yin tsafi da sasan jikinsu.
Rundunar 'yansandan jihar Oyo ta kame wasu gaggan matsafa su bakwai da suka kware wajen yin ta'anmali da sassan mutane a wani kawan gida dake wata anuguwar Soka kusa da birnin Ibadan.

Kwamishanan 'yansanda na jihar Oyo Alhaji Abdulkadiri Indabawa ya tabbatarwa manema labarai a fadar gwamnatin jihar jim kadan bayan sun kammala taron jihar. Yace mutane biyu da aka ce wai mahaukata ne sun yi ikirarin suna hada-hadar sassan mutane.

A cikin gidan da suka cafke matsafan rundunar 'yansandan ta kubutar da mutane arba'in da biyu wadanda basu da kyawon gani saboda halin da suke ciki. Duk sun rame kuma sun fita hayyacinsu. Matsafan da aka kama sun ce suna yiwa mahaukatan magani ne duk da cewa basu da alaka da gidan na Soka.

'Yansanda sun ce da zarar an kammala bincike zasu gurfanarda mutanen gaban kuliya kana kuma za'a rusa gidan. Mai baiwa gwamnan Oyo shawara na musamman kan harkoki da jama'a yace gwamnati bata da masaniya game da wurin da ake tsugunar da mutane da ake kira Soka

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar 'Yansandan Jihar Oyo ta Cafke Wasu Gaggan Matsafa - 2'06"