Femi Falana yayi furucin ne lokacin da yake nazari kan jawabin shugaban kasa da ya bayar lokacin da yake bude taron watan jiya. Yace wadanda suka jefa Najeriya cikin mawuyacin halin da ta samu kanta na cikin taron. Yace domin haka yake ganin kowa ya tashi ya fadi tabargazar da ya tafka a baya domin a samu bakin zaren gyara.
Falana yace illar barayin sata da alkalami ta fi ta masu fashi da makami. Ya kuma kalubali gwamnatin shugaba Jonathan wajen yin sako-sako da yaki da cin hanci da sata inda yace 'yan kalilan ke kwashe dukiyar mafiya rinjaye. Falana ya nuna cewa rashin gaskiyar kasar da adalci da dukiyoyin jama'a ya sa bakin duniya bai kula da samarda ayyuka ma 'yan Najeriya ba ko taimakawa harkar ilimi. Bankin na cewa 'yan Najeriya ba jahilai ba ne.
Dr Haruna Yerima daga jihar Borno yace yawancin mutanen dake cikin taron su ne suka rusa kasar, su ne suka sace kudin kasar. Su ne kuma umalubaisan duk abubuwan dake faruwa a kasar. Duk wahalar da kasar ke sha su ne suka haddasa. Yace bai ga yadda wadannan mutanen dake cikin taron zasu iya kawowa kasar masalaha ba. Yace mutane zasu yi taro ne kawai su kwashe alawus dinsu su watse ba tare da cimma komi ba. Wato kenan taron ba zai yi tasiri ba. Yanzu kowane sati biyu ana ba kowanensu nera miliyan daya da dari hudu da sittin banda mutane uku kawai da basa karba. Daga karshe yace duk abun da taron zai yi majalisun tarayya na iya yi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.