Da Muryar Amurka ya bincika, ‘yan sandan sirrin na SSS sun bayyana cewa wasu dake tsare ne ‘ya’yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram, sukayi kokarin ficewa daga inda ake tsare da su, wato shedkwatar hukumar dake daf da fadar shugaban kasa.
Jami’ar labaru ta hukumar SSS din, Marilyn Orga ta fidda sanarwar dake nuna cewa mai bayar da abinci ne ga wadannan mutane da ake tsare da su, a lokacin da yaje raba abinci, sai daya daga cikin mutanen dake tsare yayi amfani da ankwar dake hannunsa, ya bugi mutumin. A wannan lokaci ne suka yi kokarin kwace masa bindiga, amma sai ragowar jami’ai suka lura da abunda ke faruwa, sannan suka kawo dauki.
Bayanai sun nuna cewa mutane 3 ne da ake tsare da su, suka rasa rayukansu, a cikin mutum 17 dake tsare, sannan wasu sun samu raunuka.